Shugaba Buhari ya kai ziyarar bude aikin gwamna a jihar Ogun

Shugaba Muhammad Buhari ya sauka a garin Abeokuta na jihar Ogun. Buhari ya kai ziyara garin ne domin ayyukan da gwamna mai barin gado, Sanata Ibikunle Amosun, yayi.

Shugaban ya sauke garin ne da misalin karfe 10:18am, a jirgin shelikwafta mai lamba NAF 540, a filin Arcade dake sakatariyar jihar.

Ya samu tarba daga gwamnan jihar, Ibikunle Amosun, Gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Feyemi da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Ministan lafiya, Prof Isaac Adewole; Sarkin Oba Adedotun Gbadebo da tsohon mai bada shawara a jami’iyyar APC, Muiz Banire.

Daily Trust ta rawaito cewa Buhari yaki zuwa wajen bude ganuwar gari, inda ya tafi wajen manyan ‘yan siyasa da hukumomin tsaron jihar domin tattauna batutuwan da suke akwai na matsalar tsaro.

Masu Alaƙa  Mun bar barayi da Allah - Buhari

Mukarraban shugaba Buhari sun tafi wajen bude ayyukan bayan saukarshi. Daga cikin ayyukan da za’a bude sun hada da, Katafaren shagon siye da siyarwa na Adire dake Kasuwar Itoku, Dakin kallo na Amphi.


Asbitin zamani mai gadaje 250 a Oke Mosan, Filin tashi da saukar jiragen sama dake karamar hukumar Ewekoro da gidan Talabijin na Digital Studio

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: