Maimakon a shiga ‘Next Level’, matakin baya ake komawa – Hon Gudaji Kazaure

Dan Majalissa mai wakiltar karamar hukumar Gwiwa, Roni, Kazaure, ‘Yan Kwashi, a karkashin inuwar jami’iyyar APC, Hon Gudaji Kazaure yace maimakon a shiga Next Level, baya ake komawa.

Hon Kazaure a bayyana haka ne a wani taron manema labarai daya kira don yi tsokaci akan sake baiwa babban gwamnan bankin CBN jan ragamar bankin a shekaru 5 masu zuwa.

Kazaure, ya bayyana rashin jin dadinshi bisa yadda shugaba Buhari ya sake turo Gwamnan Emefele domin kara shugabantar bankin dukda matsal-tsalun tattalin arzikin da aka samu.

”Mun yadda shugaba Buhari mai gaskiya ne tare da yaki da cin hanci da rashawa, kuma munada yakini cewa zamu shiga matakin gaba ”Next Level”da mutane masu gaskiya.”

Masu Alaƙa  APC ta ci zaben shuwagabannin majalissa kamar yadda Ronaldo ya cinye Spaniya da bugun tazara - Hon Kazaure

“Amma abin mamaki, sai gashi ya (Buhari) sake zabar gwamnan ‘CBN’ Emefele a wa’adi na 2.”

“Yakamata kafin a shiga Next Level, a cire duk wasu baragurbi da suke ciki, a kawo wasu sababbi.”

Kazaure dai ya sake cewa har yanzu gwamnatin tana tuhumar Dasuki, Diziani Alisson bayan duk kudin EFCC take zargin su dashi ya fito ne daga CBN.

Hon Kazaure yayin karin haske gama da batuwa dake cewa akwai wadansu amintattun shugaba Buhari wadanda suka bashi bayanan karya game da abubuwan da suke wakana a kasa.

“Ina mamaki, akwai wadansu mutane da suke biyowa tabayan fage, suna kalamance shugaba Buhari.”

“In har aka cigaba da tafiya a haka, to maimakon a shiga “Next Level” to ba shakka sai dai a koma baya “Back Level”

Masu Alaƙa  APC ta ci zaben shuwagabannin majalissa kamar yadda Ronaldo ya cinye Spaniya da bugun tazara - Hon Kazaure

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: