Katsina: ‘Yar shekara 14 ta yanke gaban magidancin da yayi yunkurin yi mata fyade

Karatun minti 1

Yarinyar data fito daga kauyen Yargase, ta yanke gaban wani magidanci, Bashir Ya’u a lokacin da yayi yunkurin yi mata fyade.

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta bayyana faruwar wannan al’amari.

Rundunar tace ta samu rahoton ne a lokacin da aka kai Bashir, mai shekara 30 na haihuwa asibitin garin Kankara domin bashi agajin gaggawa.

Bashir, ya kai yarinyar wani dogon gini da ba’a karasa da yake kusa da kauyen na Yargase, inda daga bisani yarinyar tayi amfani da reza ta yanke gaban nashi.

Yanzu dai bincike ya kammala, kuma tini an mika takardun Bashir zuwa toku domin fuskantar hukunci kamar yadda tsarin doka ya tanada (283 Penal Code).

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog