Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya kai ziyarar bazata zuwa asibiti a garin Maiduguri da sauran ma’aikatun gwamnati.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Gwamnan Babagana bai iske ko da likita kwara daya ba a ziyarar bazatar da yayi zuwa asibitin Umaru Shehu da karfe 1 na dare.
Jaridar tace babu Likita ko daya daga cikin likitoci 19 da suke aiki a asibitin.
Sai dai ya iske Ungozomomi 10 daga cikin 135 wadanda zasuyi aiki a ranar.
Rahotan yace gwamnan ya kira Likitocin a waya domin jin bahasin dalilin rashin zuwan nasu, amma 10 daga cikinsu basu amsa wayar ba.
Haka zalika, rahotan yace gwamnan ya iske ‘yan tsirarun Likitoci a ziyarar da yakai asibitin asibitin kwararru na jihar da misalin karfe 2 na dare.
GWamnan ya bayyana rashin jin dadinshi bisa yacce ake karbar marasa lafiya a Asibitocin.
