Bincike Labarai

Wacce Kabila ce bata morar gwamnatin Shugaba Buhari?

Dukkanin manyan kabilun Najeriya suna kokawa kan cewa shugaba Muhammadu Buhari ba yi musu adalci, kodai wajen rabon mukamai ko kuma wajen yin ayyukan raya kasa.

Mutanen Yanki Arewa musamman yan jihar Kano da suke Hausawa kuma ana musu kallon manyan masoya shugaba Buhari, suna kokawa da cewa shugaban baya kulawa dasu, domin a cewarsu har zuwa yanzu babu abinda zasu dauko su nunawa duniya cewa soyayyar Buhari ce tayi musu.

Al’umma Arewa da kalibunsu sukan soki shugaba Buhari da cewa baya kula da yankinsu, dama musu aiki, har ma sukeyi masa lakabi da “Buharin Yarabawa.”

Suma a nasu bangaren, a kabilar Yarabawa, a kan samu wasu dayawa suna korafin cewa ba’ayi musu ayyukan raya kasa a yankunansu duk da cewa mutanen Arewa suna ganin sunfi kowa morar aiki.

A bangaren kabilar Igbo kuwa, ana ganin duk abinda shugaba Buhari zaiyi musu bazasu yaba ba, bisa dalilin kasancewarsu rikakkun ‘yan PDP.

Idan muka dawo bangaren rabon mukamai, dukkanin wadannan kabilun, za’a iya cewa sun sharbi roman Dimokradiyya, domin kuwa babu wacce a cikinsu bata lakume kujerun Ministoci ba.

Karin Labarai

Masu Alaka

Duk da zaman Kotun da ake yi a yau, a kan shari’ar shugaban kasa

Rilwanu A. Shehu

“Babu abinda Buhari zai iya yi akan zaben Kano” – Gwamnatin Tarayya

Dabo Online

Bama samun Wutar Lantarki sai kazo Daura – Masarautar Daura ta fadawa Buhari

Dabo Online

Malaman addinai da ‘Yan siyasa ne suka haddasa kashe-kashe a Najeriya – Buhari

Dabo Online

Buhari zai bawa matasan Najeriya aikin shuka Bishiyoyi miliyan 25

Dabo Online

Wasu manyan abubuwan da Buhari ya fada na saukakawa talaka a jawabinsa

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2