Gwamnatin jihar Borno tana shirin mayar da ‘yan gudun hijira yankunan su

Karatun minti 1

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Umara Zulum yadauki aniyar mayar da ‘yan gudun hijira yankunan su afadin jaha.

Wakilin Dabo FM a garin Maiduguri, Ibrahim Mustapha ya rawaito mana gwamnatin jihar dai takafa kwamitin sake inganta yankunan kananan hukumomi 27 na fadin jihar Borno kama daga gine rukunin gidaje da samar da ruwa da sauransu.

Ajawabinsa Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyna cewa hakika Gwamnatin sa bazata so ganin ‘yan hijira a zaune acikin gari ba duba da yadda yace mundin idan sunci gaba da zama tofa kananan hukumomin fadin jihar zasu kasance babu kowa wadda hakan zai iya karawa yan ta adda kwarin gwiwa.

Haka zalika abangaren tsaro Gwamna yace tabbas jami’an tsaro har yanzu basu dauki lamarin yaki da yan ta addan da gaske ba.

A kwamitin mayar da yan gudun hijira da Gwamna yakafa yanzu haka kwamitin karkashin jagoran cin mataimakin Gwamna, Alhaji Umar Kadafur ya jagoran ci mayarda yan yankin Kawuri, dake karamar hukumar Konduga.

An mayarda al’ummar Kawuri sama da 700 tare da bawa kowannen su naira dubu 50 da kayakin Abinci.

Abangare gudama dai yanzu haka tawagar Gwamnatin jihar sun sauka agarin Baga inda ma’aikata yanzu suke aikin gyaran wutar lantarki tare da gine rijiyoyin bursasai da sauransu.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog