//

Sarki Sanusi ya sallaci gawar Sallaman Kano

0

Ga cikakken tarihin Marigayi Sallaman Kano, Malam Aminu Dako.

Sallaman Kano Aminu Dako dan Sallaman Kano Dako an haife shi a shekarar 1945 a Lokon Zagage da ke cikin gidan Sarkin Kano, kamar yadda rahoton mu na nan Dabo FM ya bayyana.

Ya yi primary a Gidan Makama Secondary School, ya gama a shekarar 1960. Daga nan sai ya fara koyarwa a primary ta Madatai, daga nan aka mayar da shi primary ta Giginyu.

Daga nan kuma sai ya bar aikin koyarwa ya koma Native Authority sa aiki a matsayin akawu. Daga nan sai ya koma Treasury Department, daga nan sai kuma ya koma ofishin Madaki da aiki, sai kuma ya sake komawa Treasury Department.

Masu Alaƙa  Dan Majalissa a jihar Kwara ya koma ga Mahaliccinshi

A 1967 ya tafi Bidda Clerical Training Center ya yi kwas na clerical officer tsahon wata tara. Da ya dawo Kano sai ya koma Treasury Department daga nan kuma sai aka mayar da shi Medical Department.

A 1976 ya tafi Kaduna Polytechnic ya yi wani kwas akan Local Government Administration. A wannan shekarar ya tafi Tudun Wada a matsayin Executive Officer, sannan ya tafi School of Management Studies, Staff Development Center ya kara yin wani kwas na Executive Officer General Certificate.

Bayan ya gama wannan kwas din sai ya sake komawa Tudun Wada a matsayin Executive Officer General (E. O General)

Alhaji Aminu Dako ya dawo Kano Emirate Council da aiki a cikin shekarar 1984, a matsayin Private Secretary, na Sarkin Kano Ado Bayero. Mahaifin sa Sallama Dako ya yi masa sarautar Ciroman Sallama a shekarar 1993 tare da kanin sa Usman wanda shi kuma aka yi masa sarautar Galadiman Sallama.

Masu Alaƙa  Tsugunno: Masu nadin Sarki a masarautar Kano sun maka Ganduje a kotu

Alhaji Aminu Dako ya zama Sallaman Kano a ranar Alhamis, 1st January 1996, kwana daya bayan rasuwar mahaifin sa Sallaman Kano Dako.

-Dabo FM

-Wada Khalil, Nasiru (2007)
_Bayi A Gidan Dabo_: Gidan Dabino Publishers, Kano.

Allah Ubangiji Ya ji kan sa Ya gafarta masa.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020