Gwamnatin jihar Kano zata kashe naira miliyan 223 a kananan hukumomi 15 da za’a sake zabe

Gwamnatin jihar Kano karkashin ma’aikatar kananan hukumomi ta cire kudi kimanin naira miliyan 223 domin yin amfani dasu a kananan hukumomi 15 da za’a sake gudanar da zabe a 23 ga watan Maris din 2019.

Hukumar ta aike da takarda mai lamba “0623” hadi da cheque mai lamba “00000840” zuwa ga manajan bankin Unity Bank dake Sani Abacha Way domin sahalemata cire kudin. Takardar dai da samu saka hannun Darktan kula da hukumar, IBRAHIM M KABARA, da sakatare ABBA LADAN KAILANI.

Hukumar ta sake bukatar banki daya tura kudin zuwa ga asusun kananan hukumomi kamar haka:

 1. Bichi
 2. Doguwa
 3. Nassarawa
 4. Rimin Gado
 5. Gwarzo
 6. Sumaila
 7. Wudil
 8. Dawakin Kudi
 9. Kabo
 10. Dawakin Tofa
 11. Tsanyawa
 12. Kumbotso
 13. Kura
Masu Alaƙa  Har yanzu Abba Kabir Yusuf muka sani a matsayin dan takarar gwamnan PDP - INEC

Ga takardar

 

Sai dai hukumar bata bayyana dalilin cire kudin ba.

Bayan jin ta bakin masu fashin baki akan harkokin siyasa daban daban, sunyi karin haske game da fahimtarsu bisa cire kudin da cewa, za’ayi amfani da kudin ne lokutan zabe domin cimma manufar gwamnatin Kano wajen sake darewa karagar mulki karo na biyu.

Ga jerin kananan hukumomi 15 na farko

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.