PDP zataga abin girgiza rai ranar da za’a sake zabe

Gwamnan jihar Kano, Engr Abdullahi Umar Ganduje yace jami’iyyar PDP tare da magoya bayanda zasu ga abin girgiza rai a zaben da za’a sake yi a ranar 23 ga watan Maris.

Gwamnan yace jami’iyyar PDP zata sha mamaki, domin duk wata hanya da suke bi wajen yin magudin zabe sun tosheta.

“Duba da irin abubuwan da suka faru a zaben daya gabata, na siyan kuri’u da jami’iyyar PDP tayi wanda yakai ga an soke wasu guraren zabe, to a yanzu duk wannan kafar mun toshe ta.”

Da yake bada bayanin, kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba yace, har yanzu jami’iyyar su ta APC tana kan nasara kuma zasu bullo da sabon tsarin da zai kaisu ga nasara.

“Ganduje, yana nan akan matsayarshi ta tabbatar da sahihin zabe, saboda haka duk hanyar da jami’iyyar PDP ta samu wajen yin magudin zabe, ina tabbatar muku bazasu sake samun wannan damar ba, kuma zasu ga abin mamakin da zai girgiza ran su.” – Malam Muhammad Garba

“Gwamnatin Dr Abdullahi a Ganduje, gwamnati ce mai son cigaban jihar Kano, kuma da zarar an sake zabenmu zamu dora da aiyukan cigaban al’umma.”

%d bloggers like this: