Zaben2019: Ko a lahira ba abinda za’ayi idan mukaci zabe da tsiya-tsiya a Kano – Shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Hon Abdullahi Abbas yace suna nan a kan bakarsu ta cewa zasuci zaben Kano to da tsiya, ko da tsiya-tsiya.

An dai hangi shugaban jami’iyyar APC na Kano a gaban wasu matasa da ake zarginsu da bata garin da ake amfani dasu wajen tada hargitsi a wuraren zabe.

“Sojoji namu, ‘Dan Sarki naku, a wannan zaben in kun daki mutum kun daki banza, ba duniya ba, ko a Lahira ma baza’a bi ba.”

“Sai dai bamu sani ba za’a iya kai mutum Police Station, amma ina tabbatar muku kafin akai ko waye zamu sake shi. Babu zancen zuwa Bompai, ‘dan sandan daya kama idan bai sa’a ba ya bar aiki.”

Masu Alaƙa  Ganin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

“Ina tabbatar muku zamu kare mutuncinku, da darajarku. Zaben nan koda tsiya-tsiya sai munci.”

Hukumar zabe ta INEC ta dage zaben gwamnan jihar ta Kano  bisa rashin cika wasu ka’i’ogin hukumar, dalilin dayasa ta kiran zaben da wanda bai kammala ba.

Ba wannan karon ne kadai shugaban jami’iyyar na APC yayi irin wadannan kalamai ba, a baya ma kafin gudanar da zaben gwamnoni, an jiyo shi yana cewa ko da jami’iyyar PDP tayi nasara, to lallai zasu kwace nasarar su baiwa kansu.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.