Gwamnatin Tarayya ta bawa masu Aski 20 ‘yan yankin Niger-Delta tallafin Naira Miliyan 88

Karatun minti 1

Gwamnatin Tarayya ta rabawa masu sana’ar aski guda 20 ‘yan asalin yankin Niger Delta Naira miliyan 88 a matsayin tallafi karkashin hukumar dake yiwa ‘yan yankin afuwa.

Ko wanne daga cikin wadanda suka amfana da shirin, zai samu Naira miliyan 4.4 a matsayin tallafin.

A takarda mai lamba PRO/SAP&CAP/TOVO/2019/0010/V/C.1009, wacce aka aike ranar 24 ga watan Janairun 2019 daga Gwamnati zuwa ga Manajan kwafanin TOVO VICKS NIGERIA ENT. LIMITED da zaiyi kwangilar bada tallafin.

Wannan ne karo na biyu da gwamnatin take bada tallafin ma’askan a yankin.

A wata takardar dai da gwamnatin karkashin ofishin afuwa ga ‘yan Niger Delta wacce aka aikewa kamfanin MESSERS TEMONGROVE LIMITED a ranar 5 ga watan Nuwanbar 2018.

Ta nuna cewa hukumar ta ware Naira Miliyan 90, domin rabawa ma’aska 20 kudin a matsayin tallafi.

Inda su kuma kowanne daga ciki zai amfana da Naira Miliyan 4.5.

Kudin tallafin ya kunshi, kudin hayar shago.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog