Copyrighted.com Registered & Protected

Gobara a KANNYWOOD: Adam A. Zango ya zazzagi Ali Nuhu

Rigima ta barke tsakanin manya kuma fitattun jarumawa a masana’antar Kannywood, Adam A Zango da Ali Nuhu.

Ba wannan ne karon farko da jarumawan sukan samu sabani ba, saidai wannan lokaci abin yafi yin tsamari inda takai da zagi daga bangare daya.

Adam Zango ya wallafa a shafinshi na Instagram, inda yace lokaci yayi da zai fara mayar da martanin dukkan cin mutunci da akayi masa, musamman wajen zagin mahaifiyarshi.

Adam Zango ya kira sunan Ali Nuhu yana cewa “yanzu ma aka fara”

“Tinda kasa yara suka zagi mahaifiyata to kaima sai kaci Uwa*** wllh, Don uwa ba tafi uwa ba, dama na jira ne inga matakin da zaka dauka.

Kuma duk wanda ya fasa kashe ni ya raina Uwa***” – Inji Adamu Zango

Daga Shafin Adamu Zango a Instagram. Danna akan hoton domin tabbatar da sahihancinshi.
Duk dai daga shafin Zango. Danna akan hoton domin tabbatar da sahihanci.

Shima a nashi banagaren, Ali Nuhu ya mayarwa da Zango martani akan kalaman da Adamu Zango yayi.

Inda shima Ali Nuhu ya wallafa a shafinshi na Instagram yana mai cewa “An zo gun”

Daga shafin Ali Nuhu. Danna akan hoto domin tabbatar da sahihanci.

Tin ba yau ba dai jarumawa suke ta dambar wa, yayin da wasu daga cikin yaran masana’antar suke daukar bangare tsakanin jarumawan biyu.

 

%d bloggers like this: