Habibu Abubakar, dalibi a jami’ar Usman Danfodio dake jihar Sokoto, ya hadu da iftila’i bayan da ‘yan daba suka guntule masa hannu tare da kwace masa babur dinshi na hawa.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, a daren jiya Lahadi, ‘a unguwar Maina, cikin gari, ‘yan daban suka guntule masa hannu tare da kwace babur din dalibin.
Mahaifin dalibin, Mallam Attahiru Abubakar ya tabbatarwa da jaridar faruwar al’amarin.
Yace
“Abin ya faru ne da misalin karfe 2 na daren Lahadi bayan sun dana masa tarko, inda suka kwace masa babur kuma suka guntule hannayenshi. Sun barshi jini yana ta malala.”
“Anyi kokarin sanar da Kawun Abubakar da hanzari, hakan tasa aka garzaya dashi asibiti dake Wammako cikin gaggawa domin ceton rai.”
Anyi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Sokoto, amma hakar ta gaza cimma ruwa.