Gwamnatin tarayya za ta soke shirin Talabijin na ‘#BBNaija’

Gwamnatin ta shigar da korafinta zuwa ga hukumar dake kula da ‘Watsa Shirye-Shirye’ akan shirin BB Naija wanda aka fi sani da Big Brother Nigeria.

Gwamnatin ta shigar da korafin ne bayan an nuna yin Jima’i a lokacin da ake gudanar da wasan.

DABO FM ta binciko cewa tini dai gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da kamfanin Star Times domin fito da wani sabon shirin ko kuma yi wa shirin kwaskwarima.

Gwamnatin tace shirin dole shirin ya zama yana nuna tsantsar al’adar Najeriya wanda ya hada da kayan sakawa da kuma irin abincin da ake ci a Kasar.

Daraktan hukumar Al’adu da , Otunba Segun Runsewe ne ya bayyana haka a lokacin da shugabar Majalissar Mata ta Najeriya, Dakta Gloria Shoda ta kai masa ziyara.

Masu Alaƙa  Babu wani shugaba kuma 'Janar' dan damukuradiyya kamar Buhari -Yahaya Bello

Yaa bayyana cewa shirin ya sabawa dokar “Nuna Tsiraici ta 2008″. Dokar da ta haramta fito da tsiraici, ko yin wani abu daya danganci Jima i wanda mutane zasu gani.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.