Labarai

Katsina: Matasa 3 dake yiwa kasa hiduma a NYSC sun rasa Rayukansu a hatsarin Mota

Matasa 3 dake aikin bautar kasa na hukumar NYSC sun rasa rayukansu a wani hadarin Mota da ya ritsa dasu a jihar Katsina.

Hukumar NYSC ce ta tabbtar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Obemeata Alex, ya fitar a ranar Lahadi.

Hatsarin ya rista da matasan san ne a karamar hukumar Kankara dake jihar ta Katsina.

“Ranar Lahadi, 18 ga watan Agusta, 2019, ranar bakin ciki ce ga NYSC a jihar Katsina biyo bayan mutuwar Mambobinmu guda 3 a hatsarin mota a daidai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Coci a garin Funtua.

“Su 12 ne a cikin motar kirar Bas mallakar Kungiyar Mabiya Katolika dake NYSC ta Jihar Katsina.”

“A take a wajen, 3 daga cikinsu suka ce ga garin kunan.”

Ya kara da cewa; lamarin ya faru ne lokacin da gwamna yake wucewa a chan wani titin zuwa Gobirawa dake karamar hukumar ta Kankara.

Ya ce gwamnan ya tsaya tare da baiwa wata mota a cikin ta mukarrabanshi domin su gaggauta kai wadanda suke da rauni Asibiti domin karbar kulawa ta musamman. Yayin da gawarwarki aka garzaya dasu dakin ajiye gawa.

Ya bayyana cewa shugaban hukumar na jihar, Ahidjo Yahaya, ya garzaya Asibitin tare da masu manyan maaikatan hukumar domin kulawa da wadanda suka samu raunin, har ma kara da cewa suna cikin Asibitin ne motar gawar ta iso.

Karin Labarai

Masu Alaka

EFCC ta fara farautar ‘Yan Najeriya dake shiga NYSC da kwalin bogi musamman dan Kwatano

Dabo Online

NYSC ta dakatar da sansanonin bautar kasa

Rilwanu A. Shehu
UA-131299779-2