Labarai

Gwamnatin tarayya zata fara rabawa ‘yan Zamfara N5000 a kowanne wata – CCT

Anyiwa gidaje akalla 54,197 rijisata a jihar Zamfara da zasu karbi tallafin kudi na N5000 daga gwamnatin tarayya.

Temi Tope Sinkaiye, shugabar gudanarwar CCT ce ta bayyana haka a wani taron bita ga jami’an da zasu aiwatar da shirin, ranar Juma’a a garin Gusau.

Temi Sinkaiye wacce ta samu wakilcin Sadiya Abdullahi tace ‘yan Zamfara zasu rika samun kudin ne a kowanne wata daga cikin kudaden da gwamnatin tarayya take turawa kai tsaye a asusun CCT.

Tace za’a fara da kananan hukumomi 6 wadanda suka hada da Anka, Bugudu, Birnin Magaji, Kaura Namoda, Tsafe da Talata Marafa a matsayin wanda zasu fara cin gajiyar shirin.

Sashin Hausa na Premium Times ya rawaito Sadiya ABdullah ta ce; shirin na daya daga cikin tsare-tsaren tallafawa da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bullo da shi, kuma ta ke wa talakawa wajen rage musu radadin kuncin rayuwa.

“Za a bayar da naira 5,000 ce, amma kuma za a bayar da na wata biyu a lokaci guda, domin kudin su zamana sun isa wanda aka bai wa ya yi tattalin samun fara ajiye dan wani abu daga ciki domin tattalin dogaro da kai.”

Ta kara da cewa tuni hukumar ta CCT ta dauki jami’ai 137 daga cikin kananan hukumomin jihar guda 6 wadanda za’a fara dasu.

Jami’an da suka wakilci gwamnatin Jihar Zamfara sun nuna farin cikin fara wannan shiri a jihar. Sannan kuma sun sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta bada goyon baya da hadin kai wajen ganin an cimma nasarar shirin.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin Buhari zata samar da ayyukan yi miliyan 20 a zango na biyu – Minista

Dabo Online

Gwamnatin Buhari: Yawancin masu kuka sun mance 4+4, Takwas kenan ba Biyar ba -Shehu Sani

Muhammad Isma’il Makama

Najeriya ta aika rundunar sojoji 185 ƙasar Guinea Bissau domin wanzar da zaman lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Ƙurunƙus: Buhari ya hana ministoci zuwa yawon gantali ƙasashen waje

Muhammad Isma’il Makama

Daga yanzu zamu dinga bayyanawa ‘yan Najeriya kudaden su da muke kashewa a fili -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Yan soshiyal midiya ne suka dora Atiku a keken bera – Femi Adesina

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2