PDP ta kalubalanci Buhari ya bayyanawa ‘yan Najeriya kadarorinshi na gaskiya idan ya cika baya rashawa

Karatun minti 1

Babban jami’iyyar hamayya ta PDP ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mukarrabinshi, Farfesa Yemi Osinbajo kan su bayyanawa ‘yan Najeriya kadarorin da suka mallaka idan sun cika masu gaskiya.

A gefe guda kuma, PDP ta sake kalubalantar shugaban Majalissar Dattajai, Sanata Ahmad Lawan da takwaranshi, Femi Gbajabiamila, kakakin majalissar Wakilai, su bayyanawa duniya kadarorin da suka mallaka idan a har sun tabbata ba su da hannu a cikin aikata rashawa.

Mataimakin Sakataren yada labaran jami’iyyar, Diran Odeyemi, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a.

“Muna ganin ya dace Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya, Femi Gbajabiamila su bayyanawa ‘yan Najeriya irin arzikin da suka samu tun bayan shugarsu gwamnati.”

“Idan sun bayyana kadarorinsu a fili, ‘yan Najeriya za su san adadin shannun da Buhari ya ke da shi a 2019 da kuma abinda ya mallaka a 2015. Sun ce rashin tsayar da magana daya ba alama ce ta shugaba nagartacce ba.”

“Muna kira ga Buhari da sauran manyan jami’an gwamnati su kasance masu gaskiya a wurin yaki da rashawa tare da tsaftace alakar su da ‘yan Najeriya domin shi ramin karya kurare ne dole wata rana gaskiya za tayi halin ta.”

Karin Labarai

Sabbi daga Blog