(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Zaben Kano shine ma’aunin darajar INEC – Kwankwaso

Karatun minti 1
Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya ce zaben gwamna da za a kammala a jihar Kano zai zama wani ma’aunin auna adalcin gwamnati dama hukumar INEC.

Kano na daga cikin jihohi biyar da hukumar zabe ta INEC ta ce za ta sake gudanar da
zaben gwamnoni a wasu akwatina wanda ta kira da zabe mai gibi tin lokacin da aka gudanar da zaben ranar 9 ga watan Maris 2019.

Za dai a sake zaben a ranar 23 ga watan Maris din shekarar 2019.

A tattaunawar Sanata Kwankwaso da BBC gabanin zaben,  Kwankwaso ya ce zaben na jihar Kano na daukan hankulan al’ummar
Najeriya da ma wadansu kasashe.

”Wannan zabe shi zai tabbatar da darajar ita kanta hukumar zabe da gwamnati, ko kuma ya ruguje ta.’

A zaben gwamna da aka gudanar na jihar Kano, ranar 9 ga watan Maris, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da yawan kuri’u, inda ta samu kuri’u 1,014,343, inda ita kuma jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta samu kuri’a 987,829.

Sauran jihohin da za’a sake zabukan gwamna sun hadar da  Sokoto, Benue, Adamawa, da
kuma Filato.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog