Gwamnatin tarayya zata rage harajin “Giya”

Karatun minti 1

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta yi nazari dangane da harajin barasa da Kamfanukan dake sarrafa ke yi, kuma za ta duba yiwuwar rage harajin.

Wannan matakin rage harajin akan barasar ya zo ne bayan watanni 17 da gwamnatin shugaba Buhari ta karawa barasar da tabar sigari haraji da kashi 17.

A wancan lokacin, tsohuwar Ministar kudi, Kemi Adeosun ta bayyana cewa; karin harajin ga wadannan kayayyakin zai budewa gwamnatin sabon babin hanyar samun kudi, kuma zai sa a rage ta’ammuli da giyar da taba sigari wanda wannan zai rage barazanar kamuwa da cututtuka.

Sannan aka ayyana shekarun 2018 zuwa 2020, domin dawo wa teburi don sake nazarin harajin akan kayayyakin.

Rahotanni sun nuna cewa; Kamfanunnukan da suka fi yin giyar sun hada da; Anheuser-Busch InBev SA, Heineken BV da Diageo Plc wanda a halin yanzu suke fama wajen siyar da kayayyakin, inda suka bukaci gwamnati da ta yi duba ga yiwuwar rage harajin don cinikinsu ya samu ya bunkasa.

Paul Abechi mai magana da yawun Ministar Kudi, Zainab Shamsuna ta bayyana cewa; akwai yiwuwar rage harajin duba da yanayin da Kamfanunnukan suka fada.

Rahotan Jaridar Leadership Hausa

Karin Labarai

Sabbi daga Blog