Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Abdulaziz, tace zata dauki matsafa 1,700 domin samarwa jihar zaman lafiya.
Gwamnatin ta bayyana haka ne ta hannun Kwamishinan kananan hukumomi na jihar, Alhaji Bello Dankande, a wani taro da yayi da Sarakunan gargajiyar jihar.
“Kowacce masarauta zata samu mutum 100 hadi da 500 da muka dauka daga farko. Zamu girke wasu a gidajen mai domin hana ‘yan bindigar samun mai.
Yace Gwamnatin bazata lamunci a cigaba da tashin hankali a fadin jihar ba.
“Abin ya isa haka, bazamu bari a cigaba da wannan kisan kiyashi da akeyi a jihar mu ba.”
“Gwamnatin tarayya data jiha nayin iyakacin kokarinta na yaki da ‘yan ta’addar.