Mutane sun yi yunkurin afka wa Rumbum Abincin Tallafin Korona na jihar Bauchi

Karatun minti 1

Wasu da ba a san ko suwaye ba, sun yi yunkurin afka wa rumbum da gwamnatin jihar Bauchi ta ajiye kayan abincin jihar na tallafin Korona a yau Lahadi.

Gwamnan jihar, Bala Muhammad ne ya sanar da haka a shafinsa na Facebook.

Sai dai Gwamnan ya ce da suka zo basu samu komai ba domin a cewarsa gwamnatin jihar ta riga ta rabar da kayan gaba daya.

“An sanar da Shugaban ma’aikatana, ya bayar da umarnin a bude rumbum. Da aka bude, sun shiga sai suka juya suka tafi saboda babu komai a ciki. Hakan ya faru ne saboda mun rabar da komai da komai.”

“Don sauke nauyi, watanni baya da muka fara rabon kayyakin, na hada wani kwamiti da ya kunshi ni da kai na, mataimaki na, shugaban jami’iyyar PDP na jiha da na sauran kafatanin jam’iyu har da shugabannin gargajiya da sauransu.”

Tin dai bayan da zanga-zangar ENDSARS ta ja baya, al’ummar wasu jihohin Najeriya suka yi ta fasa rumbunan da aka ajiye kayan tallafin Korona. Kayan da ake tunanin an basu tin watan Maris basu raba ba.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog