Gwamnoni zasu fidda mutane miliyan 24 daga Talauci zuwa shekarar 2030

Gamayyar kungiyar Gwamnonin Najeriya, NGF, ta shirya fitar da ‘yan Najeriya 24 daga kangin Talauci.

Gwamnonin sun bayyana shirinsu na yin hadin gwiwa da gwamnatin tarayya domin tabbatar da wannan shiri kafin shekarar 2030.

Shugaban sashin labarai na kungiyar, Abdulrazak Bello Barkindo, ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a babban birnin tarayya Abuja.

Bello Barkindo ya bayyana cewa kungiyar gwamnoni ta hada gwiwa ne tare da ofishin mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osibajo.

Yace an tini dai shirin ya fara ranar Litinin a jihar Kaduna tare da sa ran kammala shi a jihar Ekiti.

Masu Alaƙa  Kotu ta kori bukatar haramtawa Ibrahim Magu zama shugaban EFCC

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.