Yan soshiyal midiya ne suka dora Atiku a keken bera – Femi Adesina

Mai bawa Shugaba Muhammad Buhari shawara kan yada labarai, Femi Adesina ya lissafa wasu tarin kashe-kashen mutane ta yace sune suka dora dan takarar jamiyyar PDP, Atiku Abubakar a keken bera.

Dabo FM ta jiyo Mr Femin yana wannan ikirarin ne a wata wallafa da yayi a shafukan sa na sada zumanta, inda cikin lissafin sa ya lissafo harda yan turin jeka ka mutu na soshiyal midiya, inda yace su suka tatike atiku tas.

“A wata ‘kididdiga da akayi ta nuna cewa yan soshiyal midiya ba wata rawa da suka taka cikin zaben Atiku, gudun mawar kashi 9 zuwa 11 cikin dari kawai suka iya tsinanawa a zaben daya gabata.”

Masu Alaƙa  Kotu ta kwace kujerar dan majalissar APC ta bawa na PDP a jihar Imo

A lissafin mai bawa shugaban kasa shawara, Femi Adesina ya fara da lissafo Shugaba Obasanjo sannan yaci gaba da jero su kamar haka, yan ‘Atikulators’ wanda yace wadannan sune yan fasa-fasa musha ruwan kwai.

Yaci gaba da cewa akwai Malaman addinai musamman fastoci sune suka zama yan duba da suke gayawa Atikun abinda zai faru gaba, sai kuma yan siyasa, masu kudi da sukejin zasu iya chanja kowa, lauyoyi da dai sauransu.

“Yanzu da kotu ta kori karar na rasa ina Atiku zai dosa, Kotun Duniya? Naji wasu na cewa kawai ya tafi kotun kwallon Tenis wato ‘Tennis Court’.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.