Habib4u: Dattijon daya bukaci Hanan ta tura masa hotonta mai motsa sha’awa

dakikun karantawa

Binciken DABO FM ya bi dindigi wajen binciko sunaye da kuma hotunan wadanda ake zargi dayin tarayya da Fatima Musa duk da sunsan cewa matar aure ce.

Daga cikin wadanda ake zargi da magana da Hanan duk da tana da aure, akwai masu amfani da manhajar Instagram masu suna @Habib4u da @6affa.

DABO FM ta shiga manhajar Instagram don neman masu sunaye da hotunan suka nuna dasu Hanan take magana duk da tanada aure.

DABO FM ta fara binciken ta akan @Habib4u a shafin Instagram, inda wakilanmu suka bincika sunanshi Ahmad Habibu.

Bayan shafe binciken mu akan shafin @Habib4u, a dai dai lokacin bincikenmu, yana da mabiya 1,231 inda shi kuma yake bin 2,032.

Daga cikin wadanda Ahmad Habibu @Habib4u yake bi tare da suma suna binshi, sama da kaso 70-80 dukkanin su mata ne.

Sai dai kafin wallafa wannan rahoto, da safiyar Talata, mun samu cewa, tini dai aka chanza hoton da yake kan farfajiyar mai shafin tare da mayar da shafin ‘Private’ (Babu wanda zai iya ganin abinda ya kunshi shafin sai mai shafin ya yarda tare kuma da goge hotuna 121.

A dai dai wannan lokacin da muka hada wannan rahoto kuwa, tini dai aka goge shafin daga kan manhajin Instagram.

Sai dai DABO FM tana da hotunan Ahmad Habibu wanda da ake zarginshi da zama daya daga cikin musabbanin lamarin zargin Hanan da caccakawa Sa’eed mijinta wuka a ciki.

An zargi Ahmad Habibu da yin zantuka banza tare da Hanan wanda har ya bukaci ta tura masa hoton ta mai motsa sha’awa a Instagram.

Zamu kawo muku hotunanshi a nan gaba kadan.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog