(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

‘Yan Shi’a sun harbe jami’an tsaron dake gadin majalissar tarayya

Karatun minti 1

Kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Najeriya, wacce aka fi sani da Shi’a sun harbe jami’an yan sanda dake gadi a majalissar taryyar Najeriya.

Sashin Hausa na jaridar Premium Times ya rawaito cewa ‘yan kungiyar Shi’ar a ranar Talata, sun harbe ‘yan sanda guda 3 dake gadin majalissar tarayyar Najeriya a cigaba da gudanar da zanga-zanga da sukeyi.

Premium Times ta rawaito cewa masu zanga-zangan sun harbe ‘yan sandan ne a daidai lokacin da suke kokarin tare su daga kutsawa cikin zauren majalissar.

Wakilin Premium Times ya tabbatar da cewa daya daga cikin jami’an da yan Shia suka harbe ya rasa ranshi a nan take inda kuma aka garzaya da sauran 2 asibiti.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog