(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Kano: Alakar ‘Yan Kwankwasiyya da Propaganda, Daga A.M.D

dakikun karantawa

Tafiyar Kwankwasiyya tafiya mai karfin matasa wacce Dr Rabi’u Musa Kwankwaso yake jagoranta.

Sani kowa ne cewa, a wannan kadamin da muke ciki, hanyoyin samun labarai nada sauki saboda shigowar ‘yan social media musamman ta kafar Facebook.

Mabiya Kwankwasiyya mutane ne masu yawa, wanda suka bi suka shiga shafunan sada zamunta musamman na Facebook, suke rubuto labaran da suka ga dama saboda tasirin magan-ganunsu.

A ina dan bincike na, na gano ‘yan Kwankwasiyya mutane ne masu yada farfaganda, daga cikin abubuwan da suke yada na rudu sun hada da:

  1. Karin kudin aikin Hajjin 2019 zuwa Miliyan daya da dubu dari takwas, wanda hukumar alhazai ta karyata.
  2. “Magana akan lauyoyi dari da suka shirya wanda Audu Bulama zai jagoranta wajen kwatowa Abba kujerar Gwamna.”
  3. Bidiyo da suka ce suna dashi wanda aka baiwa DIG, AIG, REC INEC cin hanci wajen bari ayi magudi a zaben Kano.
  4. Bidiyo da suka ce suna dashi wanda mai girma Gwamnan Kano yana aikata wani abu da addini ya hana.
  5. Zuwan Asiwaju Bola Tinubu, El-Rufa’i da wasu gwamnoni na jihohin da APC ke mulki, wanda dukkanin wadanda suke ambata kowa ya fito ya karyata.
  6. El-Rufa’i ya mutu, Direban El-Rufa’i yayi mumunan hadari.

Wadannan sune wanda na tsakuro domin fada, zuwa wani dan lokaci kuma zan sake rubuto wasu.

Saboda irin wadannan Propaganda ta yan Kwankwasiyya yasa wasu suke kin yadda da hotuna da bidiyon da suke yadawa na zaben Kano, ko dai ace ba Kano bane, ko kuma ace abin ba lokacin zabe ya gudana ba.

Ya zamana cewa a yanzu ‘yan Kwankwasiyya sunma fi wasu jaridun Najeriya labarai irin na kanzon kurege.

Akwai wata kyakkyawar alakar mutunci dake tsakanin Kwankwasiyya da propaganda.

Wannan shine karo na daya, na biyu na fitowa nan bada jimawa ba.

Karanta kashi na biyu anan

Karin Labarai

Sabbi daga Blog