//
Wednesday, April 1

Har yanzu ina cikin dimuwar saukalen da kotin koli tayi min -Tsohon Gwamnan Imo

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsohon gwamnan jihar Imo da kotin koli ta tsige cikin satin nan, Emeka Ihedioha ya bayyana cewa ya girgiza da hukuncin kotun koli tayi akan sa na tsige shi a matsayin gwamnan jihar.

Dabo FM ta jiyo Ihedioha yana bayyana hakan ne a lokacin da shugaban cin jam’iyyar PDP karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya kai masa ziyarar jaje a gidan sa dake babban birnin tarayya Abuja. Kamar yadda TheCable ta fitar.

Kotun kolin dai ta bawa dan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodinma kujerar gwamnan jihar Imo ne kwanaki kadan da suka gaba ta.

Ihedioha ya kara da cewa hukuncin yafi karfin jihar Imo, wannan shine manunin siyasa da zabukan najeriya a nan gaba.

Masu Alaƙa  Dama can nasan Ganduje ne yaci zaben Kano -Buhari

Tini dai Jam’iyyar PDP tayi watsi da hukuncin kotun kulin.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020