//
Wednesday, April 1

Yayin da take yi wa Maza illa, ‘Agwaluma’ tana yi wa mata maganin cutar cizon Sauro

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Bayan bincike da masana lafiya sukayi akan illar da ‘Agwaluma’ take yi wa Maza na rage musu karfin jima’i, binciken ya tabbatar da babban al’fanunta ga jikin iyaye Mata.

DABO FM ta tattara cewa masanan sun bayyana cewa, Agwaluma tana dauke da wasu sunadarai wadanda ke hana bunkasar cutar cizon Sauro a jikin Mata musamman a lokutan da suke dauke da juna biyu.

Masanan sunce a yayin da mata suke dauke da juna biyu, yiwuwar kamuwa da cutar cizon Sauro yana karuwa da kaso mai yawa a jikinsu, wanda ya kan kawo barazana ga lafiyar abinda yake jikinta. Sun bayyana shan agawaluma a matsayin wani riga kafi da zai hana kamuwa da cutar tare da warkar da ita idan ta rika ta shiga jiki.

Masu Alaƙa  Kiwon Lafiya: Mata suna gane namiji mai karyar Ido na ganin Ido - Binciken Kwakwalwar

Binciken da aka wallafa a mujallar Anc Sci Life ta 2017, ya tabbatar da kwallon agwaluma yana dauke rage kamuwa da cutar ‘Malaria’ da kaso 72.97 zuwa 97.30, yayin da naman agwalumar yake rage kamuwa da cutar da kashi 72.97 zuwa 81.08.

DABO FM ta tattara cewar sashin harhada magunguna na jami’ar Nmadi Azikiwe dake jihar Anambra yace kwallon agwaluma da namanta yana rage kamuwa daga cututtukan da kwaruka suka saka wa jikin dan adam da kaso 96.10.

Daga karshe masanan sun amince da yin amfani da agwaluma a matsayin rika kafi da kuma maganin cutar ‘Malaria’

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020