//
Wednesday, April 1

Hoton ‘soyayya’ na Baturiyar Amurka da dan Kano a dakin Otal ya janyo cece kuce

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hoton Sulaiman da masoyiyarshi yar kasar Amurka a dakin wani Otal a jihar Kano, ya janyo cece kuce tsakanin mutane musamman a kafofin sada zumunta.

Tin bayan zuwan tsohuwar baturiya mai shekaru 43 Kano domin kawo wa masoyinta matashi Sulaiman wanda har ta kai ga fara shirin aure, al’umma da dama suke ta tofa albarkacin bakinsu.

Sulaiman tare da Madam Sanchez yayin daukar hoto irin na masoya.

Lamarin yayi tsamari bayan fitowar hotunan wanda yasa wasu ke ganin yakamata a daura auren kafin lokacin da aka shirya daurawa bisa ganin illar da take tattare da barinsu suna zama a dakin Otal su kadai.

Mutane da dama na cewa; “Ayi maza a daura auren nan kafin ta lalata yaron nan.”

Masu Alaƙa  Sashin Jami’ar ABU Zaria ya baiwa Anas Umar mai hoton Sarkin Kano Sunusi II lambar yabo

DABO FM ta tattara cewa bayan tattauanawa da iyayen matashin, an tsara dauri auren a cikin watan Maris mai kamawa.

Haka zalika a bangaren mahaifin matashin, Alhaji Isa Sulaiman tsohon jami’in yan sanda, ya gindaya wa baturiyar sharuda wadanda a cewarshi dole ta cikasu kafin a daura auren.

Sharudan da suka hada da; kawo rubutacciyar sahalewar auren daga iyaye ko waliyyanta, barin matashin ya cigaba da fadada karatunshi, barinshi a addininshi tare da saka jami’an tsaro da gwamnati a cikin lamarin.

Tini dai baturiyar ta amince da sharudan tare da bayyana shirinta na komawa Amurka a cikin wannan makon domin kammala shirye-shirye kafin lokacin auren na watan Maris ya kama.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020