Labarai

Matashin da yafi kafatanin mutanen duniya gajarta ya mutu a kasar Nepal

Mista Khagendra Thapa Magar, matashin da akayi ittufakin yafi mutanen duniya baki daya gajarta a duniya ya mutu a wani asibiti dake kasar Nepal.

DABO FM ta tattara cewa matashi ya mutu yana da shekaru 27 kacal a duniya.

Da yake tabbatar da al’amarin, dan uwan matashin, Mahesh Thapa Magar ya fadawa AFP cewar ya sha fama da cutar Lumoniya, inda suka ce a wannan karon, zuciyarshi ta tabu.

Matashin mai tsawon santi mita 67.08 ya mutu a asibitin garin Pokhara, nisan kilomita 200 zuwa birnin Kathmandu, babban birnin kasar Nepal.

Tin dai a shekarar 2010, Mista Khagendra ya samu shaidar mutum mafi gajarta a duniya a dai dai lokacin da yake bikin murnar cika shekaru 18 a duniya.

Sai dai ya rasa kambun ne bayan da aka gano wani wanda yafi Khagendra tsawo mai suna Chandra Bahadur Dangi dan kasar ta Nepal da yake da tsawon santimita 54.6.

Bayan rasuwar Mista Chandra a shekarar 2015, Mista Khagendra ya sake samun kambun mafi gajarta a duniya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya mutu

Rilwanu A. Shehu

Sanata Imo ta Arewa ya mutu bayan faduwa a bayan gida

Dabo Online

Shugaban limaman Juma’a na Kano, Sheikh Fadlu Dan Almajiri ya rasu

Dabo Online

Sakataren Kungiyar ‘Yan jaridu ya yi rashin mahaifiya

Mu’azu A. Albarkawa

An binne Dalibin da ya rasu jim kadan bayan kammala Digirinshi na 2 a kasar Indiya

Dabo Online

Alhaji Shehu Shagari ya cika shekara 1 da rasuwa

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2