Labarai Siyasa

Kotun Koli: Farfaganda baza ta canza abinda Allah ya tsara ba -Abba ya yiwa Ganduje martani

Dan takarar gwamna a jamiyyar PDP ta jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif ya bayyana babu wata farfaganda da zata firgita shi a kan shari’ar zaben gwamnan Kano daya shigar a gaban kotun kare kukan ka.

Rahoton da Dabo FM ta samu daga jaridar PoliticsDigest ya bayyana wannan kalamai sunzo ne a martani bisa kalaman gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda Ganduje ke cewa babu wata kamanceceniya a shari’ar Kano da ta jihar Imo.

Abba Kabir Yusif ta bakin mai magana da yawun jam’iyyar PDP ta jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin-Tofa yace “Yanzu baza mu ce komai ba tunda magana tana gaban babbar kotun koli har sai Litinin munga an yanke hukunci, kuma muna kyautata zaton kotu zatayi adalci.”

Sunusi ya kara da cewa “Mu mutane ne masu bin doka don haka baza muyi magana akan abinda ke gaban kotu ba, amma muna fatan zaayi adalci kan fashin zaben da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Inec da jamian tsaro suka yi.”

“Kuma muna kara yin amfani da wannan dama don yin godiya ga magoya bayan mu na Kano har ma na sauran jihohi bisa addu’o’i da fatan alkhairi da suke mana a wannan shari’ar da muke neman hakkin mu.”

Tini dai yau take ranar jajiberin yanke hukuncin shari’ar da dan takarar jamiyyar PDP, Abba Kabir Yusif ya shigar domin kalubalan tar kujerar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a kotun kare kukan ka.

Karin Labarai

Masu Alaka

Gwamnatin jihar Kano zata fara biyan albashin N30,000

Dabo Online

Ganduje ya siyo motoci kalar ‘Kwankwasiyya’ guda 100 na zirga-zirga a jihar Kano

Dabo Online

Mata sunfi Maza rikon amana, na tabbata bazasu hada kai don a kifar damu ba – Ganduje.

Dangalan Muhammad Aliyu

Mun barwa Allah komai shiyasa hankalinmu yake kwance kan batun Shari’ata – Abba Gida Gida

Dabo Online

Kotu ta kwace kujerar Dan Majalissar tarayya na APC ta bawa PDP a Kano

Dabo Online

Rikicin Siyasa: Ganduje ya sake gina Masallacin da Kwankwaso ya rusa

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2