Hukumar kare hakkin dan Adam ta duniya ‘IHRC’ ta baiwa Saraki aikin jakandancinta na musamman

Hukumar dake rajin kare hakkin bil adama ta duniya ta baiwa shugaban majalissar Dattijai, Dr Bukoula Saraki aiki a matsayin babban jakadanta na duniya.

Sanarwa data fito daga ofishin yada labaran shugaban majalissar, tace hukumar ta aikewa Sarakin takardar neman yardar shi kan aikin da hukumar tin ranar 16 ga watan Maris din 2019.

“A cikin wata wasika da aka aike ranar 16 ga watan Maris, Babban jami’in Diplomasiyya na Najeriya da wasu kasashen Afrika, Ambasada Friday Sani ya ce, bisa amincewar sakataren hukumar IHRC, an nada Dr Bukuola Saraki a matsayin daya daga cikin jakadunta mai girma kuma na musamman.”

Aikin Saraki ya hukumar zai kasance wanda zai jagoranci tawagar jami’an Diplomasiyyar hukumar a ayyukan da zata gudanar na duniya baki daya.

Ranar 10 ga watan Afirilun 2019, Dr Saraki ya sanya hannu a takardar shaidar amincewa da aikin da hukumar ta bashi.

Ya kuma nuna jin dadinshi da godiya bisa aikin da hukumar ta bashi.

%d bloggers like this: