Labarai

Indiya: An kama dan Najeriya da Hodar Iblis “Cocaine” a kasar Indiya

Hukumar yan sanda a kasar Indiya ta cafke wani dan Najeriya dauke da miyagun kwayoyi.

Dan Najeriyar mai suna Ikenna ya kasancewa yana zama ne a kasar ta Indiya ba bisa ka’ida.

An dai kama Ikenna a jihar Delhi, daren Lahadi 14 ga watan Afirilun 2019 da kwayoyin “Crystal Meth” mai nauyin gram 10, wanda yayi ikirarin ya siyo ne daga jihar Mumbai.

Bayan kame shi a akan hanyarshi ta  zuwa wani wajen Party inda yake siyarwa, ‘yan sanda sun tisa keyarshi zuwa gidan da yake zauna a unguwar Kardampuri.

Yan sanda sun kama Hodar Inblis “Cocaine” mai nauyin gram 18 a gidan da yake zaune haya.

Tin shekarar 2013 wa’adin zaman Ikenna a kasar Indiya ya kare, hukumar yan sandan sunce ya shigo kasar ne a matsayin dan wasan kwallon kafa.