Kotu ta ruguje nadin Sarakuna 4 da Ganduje yayi a jihar Kano

Karatun minti 1

Babbar kotun jihar Kano dake zamanta a karamar hukumar Rano tayi fatali da karin masarautun yanka hudu da gwamnatin jihar Kano ta samar a makon da ya gabata.

Gidan Rediyon Arewa dake a jihar Kano ya rawaito cewa ; Kotun ta yanke waannan hukuncin ne a zamanta na yau Laraba.

AB Mahmoud, lauyan masu kara ya koka kan yadda tsagin gwamnatin jihar Kano ta bijirewa umarnin da kotun ta bayar na dakatar da tabbatar da sarakunan a ranar 10 ga wata.

Mai Shari’a Justice Nasiru Saminu yayi fatali da masarautu 4 da gwamnatin ta samar inda kuma ya jaddada cewa babu wata halastacciyar masarauta a Kano face masarautar Kano da Sarki Sunusi yake jagoranta.

An dai dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin da za’a shiga.

Tin dai a ranar 8 ga watan Mayu ne gwamna Ganduje ya rattaba hannu a bisa dokar da majalissar jihar tayi a cikin kwana 2.

Sai dai Gandujen ya ketare wani hukuncin wata babbar kotun tarayyar dake da zama a Ungoggo wacce ta bukacin gwamnatin ta dakatar da nadin tare da kin basu takardun kama aiki a hukumance.

Al’umma dayawa suna fassara karin masarautun bisa kudirin da gwamnan yake dashi na rage darajar Sarki Muhammadu Sunusi II.

Hakan na zuwa ne bayan da tsagin gwamnatin suka zargeshi da goyon bayan jami’iyyar PDP a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog