Manyan Labarai

NDLEA ta kai sumame Sakatariyar Jam’iyyar APC ta jihar Jigawa, tayi ram da wasu

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen jihar Jigawa ta ce ta kama diloli tare da masu amfani da kayan maye 16 a cikin garin Dutse, babban burnin jihar Jigawa.

Mataimakin shugaban hukumar a jihar Jigawa, Mista Oko Michael, ya tabbatar da kama mutanen ga manema labarai.

Ya ce; An kama masu laifin ne a harabar hedikwatar jam’iyyar APC da ke cikin garin babban birnin Dutse.

Mista Oko ya bayyana cewa jami’an hukumar NDLEA sun kai samame wurin ne ranar Lahadi bayan samun korafi daga jama’a a kan yadda batagari suka mayar da wurin cibiyar sha tare da hada-hadar kayen maye a wurin.

“Mun kai samame wurin ne bayan mun samu korafi da dama daga wurin jama’a a kan yadda wasu batagari suka mayar da harabar hedikwatar jam’iyyar APC da ke Dutse, babban birnin jiha, ciyar sha da fataucin kayen maye,” a cewarsa.

Ya bayyana cewa an samu kullin tabar wiwi yayin da aka kama matasan tare da bayyana cewa za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binncike.

Sakataren yada labaran jam’iyyar APC a jihar Jigawa, Alahji Nasiru Dahiru, ya tabbatar da kai samamen da jam’an hukumar NDLEA suka yi, amma ya musanta cewa masu laifin mambobin jam’iyyar APC ne.

Karin Labarai

Masu Alaka

Yanzu Yanzu: Masu garkuwa da mutane sun sace matar dan majalisa a Jigawa

Muhammad Isma’il Makama

‘Yan bindiga sun hallaka mutane a jihar Jigawa

Dabo Online

Rikicin Fulani yayi sanadiyyar rasa rai a jihar Jigawa

Rilwanu A. Shehu

An kashe Manomi sakamakon rikicin Fulani a jihar Jigawa

Rilwanu A. Shehu

Amarya ta gamu da Ajalinta a Hanyar gidan Miji

Rilwanu A. Shehu

Gwamnatin jihar Jigawa zata fara biyan albashin N30,000 a watan Disamba

Hassan M. Ringim
UA-131299779-2