Da safiyar yau ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya kai ‘danshi Abubakar, makarantar Firamare ta Capital School dake jihar.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan ya alkaurata sanya ‘dan nashi a makarantar gwamnati da zarar ya cika shekaru 6 a duniya.
Sai dai DABO FM tayi waiwaye wajen dubo irin ayyuka da gwamnan yayi a makarantar a watanni 17 da suka gabata, kama daga inganta ajujuwa da kawo ingantattun Malamai masu kwarewa.
A ranar 13 ga watan Maris, 2018, Kwamishinan Ilimi na jihar a wancen lokaci, Ja’afaru Sani, ya tabbatar da mayar da malamai 42 da suke aikin wucin gadi a makarantar suka zama Malaman din-din-din.
Haka zalika, gwamnatin ta bayyana gyaran Makarantar akan kudi na Naira miliyan 195 domin mayar da ita cikin jerin Makarantun da suka fi kowanne a fadin Najeriya. – Daily Trust, PM News, SignalNG da Majalissar kula da ayyukan raya kasa ta jihar KDMobp sun tabbatar da haka.
Hakan ce tasa wasu suke alakanta gyaran makarantar duk a cikin shirin saka danshi domin yin karatu a ciki.
Hasalima dai Makarantun “Capital Schools”, ba makarantu ne irin na gama-gari ba, domin kuwa ‘dan talaka bazai iya karatu aciki ba saboda tsadar ta.
A wata hira da sashin Hausa na BBC yayi da shugaban Makarantar, ya bayyana kudin da kowanne yaro yake biya a matsayin kudin makaranta a kowacce shekara.
A halin yanzu, iyaye suna gagara ture ‘ya’yansu Makarantun da ake biyan N750 kacal.
A jihar Kano, akwai Makarantar ‘Kano Capital School, itama makarantace da ‘dan talaka baya iya shigarta domin tsadarta.
