0
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa, inuwar jami’iyyar, Sowunmi yace Alhaji Atiku Abubakar bazai taba samun nasarar zabe ta halartacciyar hanya ba.
A wani faifan sauti na sirri da mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari ya wallafa a shafinshi na sada zumunta, Fetus Keyamo.
Har ila yau ba’a san yaushe Sowunmi yayi maganar ba amma dukkanin alamun sun tabbatar da anyi maganar ne a cikin watan da muke ciki na Fabarairu, kwanaki kadan da suka rage a gudanar da babban zaben kasar.
Kwanaki hudu suka rage, a shirye shiryen gudanar da zaben shugaban kasa.
