Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Zamu nuna ba-sani ba-sabo akan Sarakuna da sauran masu hannu cikin kashe-kashe a Zamfara -Gwamna Matawalle

1 min read

Gwamnatin Zamfara ta ce a shirye take ta aiwatar da shawarwarin kwamitin da ta kafa wanda ya gudanar da bincike game da matsalar ‘yan bindiga da satar mutane da suka addabi jihar.

Kwamitin dai ya bayar da shawarwari 132 kuma daga cikinsu akwai shawarar tube wasu sarakunan gargajiya 5 da hakimai 33, wadanda kwamitin ya zarga da hannu dumu-dumu cikin al’amarin matsalar tsaron Zamfara.

Kamar yadda kuka ji a rahoton da Dabo FM ta kawo muku, cikin wadanda kwamitin ya lissafo akwai kuma jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kwamitin ya zarga tare da bayar da shawarar a hukunta su.

Yusuf Idris Gusau daraktan watsa labarai na gwamnan jihar, Bello Matawalle, ya shaida wa BBC cewa gwamnan ya karbi rahoton kuma ya yi alkawalin aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar.

Sai dai ya ce gwamnati za ta fara ne da shawarwarin da ke bukatar daukar matakin gaggawa.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.