Sharhi

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

-Muhammad Aliyu

Sace Yara guda 9 ‘Yan jihar Kano, aka siyar da su aka kuma mayar dasu Kiristoci a jihar Anambra – Lamari mai daukar hankali daya kamata ace Musulmi musamman na Arewacin Najeriya yafi maida hankali wajen kin jini da kuma neman gwamnati ta shiga ciki al’amarin.

Sai dai abin takaici, yacce al’ummar Musulmi na kafafen sadarwa da suke kiran kansu masu kishin musulunci sun gaza cewa komai.

Daga cikin dan binciken da na gudanar, na gane cewa; dayawa daga cikin masu ikirarin kishin Musulunci a kafafen sadarwa, basu nuna alhininsu akan lamarin ba.

A bangaren Malaman Kafafen sada zumunta kuwa, wadanda suka saba fitar da bidiyo da zarar wani abu ya faru da cewar su ta “An ci mutuncin Addini”, har yanzu sun gaza cewa komai duba da cewa wannan lamarin, abune da ya kunshi yiwa addinin Allah zagon kasa.

A ina tunani, abinnan daya faru, abune daya kamata dukkaninmu mu tashi tsaye wajen dakile faruwarshi anan gaba.

Nayi imani cewa adadin Yara 9 da rundunar ‘yan Sanda ta kubutar bai kai ko kashi 0.5 na cikin Yaran da aka dauke a jihar Kano ba, ba a iya jihar Kano ake wannan ta’asar ba.

Suma a bangaren gwamnatocinmu na jihohin Musulunci da jami’an Gwamnatin Tarayya, suna tsoran yin magana mai karfi akan hakan domin kar ace su sun fiye nuna addini ko kuma suma son kawo rabuwar kasa ta hanyar daurawa mutanen wani addini laifi. -Fahimta ta.

Meyasa muka bari siyasa tayi mana tasiri dayawa haka? Da har zamu hadu da murya daya mu kushe wani abun da wata tafiyar siyasa wacce ba tamu ba tayi amma wajen yin murya daya don kare hakkin Allah sai ya gagaremu?

Babu wanda zai tashi ya taya mu kai kukan mu ga hukuma, ko kuwa jira mukeyi har sai ‘yan Uwanmu na Kudu sun taya mu? Su da suke karyata labarin dan kare addinsu a kabilunsu.

Meyasa matsalar Arewa bata zama matsalar da kasa take dubawa?

Babban makasudin shine rashin tsayayyun kafafen watsa labarai da suke kare muraden yankin.

Misali; Ko a wannan al’amari, har ila yau, Jaridar Daily Nigerian ce kadai ta fitar da rahotan – Jaridar da itama siyasa yasa wasu na mata kallon bata fadar gaskiya.

Hakan yana daga cikin halayyar dan Arewa, mu ki namu wadanda su suke bamu goyon baya, mu so wadanda kullin burinsu muyi kasa.

Matsalar Arewa bazata zama matsalar da za’a saurara ba har sai mun samu kafafen yada labarai tsayayyu wadanda zasu rika wallafa labaran da zasu kare muradan mu.

A shekarar 2016, da wata Ose Oruru, ta biyo wani masoyinta daga kudancin Najeriya zuwa Arewacin Najeriya, kafofin watsa labaransu suka kambama lamarin da har ta kai sun addinantar da al’amarin.

Duk da cewa ita Oruru ta bayyana cewa ta biyo masoyin nata bisa rajin kanta kuma bashi da hannu a ciki, wadannan kafofi suka mayar da abin addini wanda har yau a haka ake kallo.

Mu kuwa a Arewa, an barmu da kwarancewa wajen tsinewa shuwagabanni da aike-aiken sakonni da bazasu amfane mu ba.

Kaico!

Karin Labarai

Masu Alaka

#Xenophobia: Abin kunya ne shugaba Buhari ya ziyarci kasar Afirika ta Kudu – Usman Kabara

Dabo Online

Ko dai a dawowa da Sultan alfarmarsa, ko ya zare hannunsa a komai, Daga Hassan Ringim

..

‘Idan Malamai na Allah basu farga ba, shedanun malamai za su cefanar da Musulunci’

Dabo Online

Meyasa wasu mutane suke jin tsoron tofa albarkcin bakinsu wajen kawo gyara a siyasa?, Daga Umar Aliyu Musa

Dabo Online

Alakar dan Majalissar tarayya na Fagge da Al’ummar da yake wakilta, Daga Umar Aliyu Fagge

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani
UA-131299779-2