Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Muna sa ran sabbin Sojoji zasu iya tunkarar kowanne kalubale – Gen Sani Muhammad

2 min read

A wani bangare na bukin yaye sabbin Kuratan Sojoji da Makarantar horas da kwaratan soji ta Kasa dake Zariya ke shirin gudanarwa a ranar Asabar 19 ga watan Oktoban nan, ta gudanar da taron raba kyaututtuka ga wasu daga cikin wadanda suka yi fice, a lokacin horas da sabbin daukar karo na 78, taron, wanda aka gudanar a filin fareti na Hama Kim dake harabar Makarantar, ya samu halartan Al’ummar daga ciki da wajen Makarantar.

A jawabin sa, babban kwamandan Sojin kasa na Kasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, wanda Major Janar Aminu Bici mai ritaya ya wakilta, ya bayyana gamsuwar sa da irin horon da nau’in Jami’an da Makarantar ke yayewa a koda yaushe, kuma ya yi fatan samun karin sojoji masu kishin Kasa da burin su shi ne cigaban Najeriya da Al’ummar ta.

Ya hori Jami’an da za’a yaye a ranar 19 ga watan Oktoban nan, su kasance masu cigaba da aiwatar da horon da suka samu tare da fadada ilimin su ta hanyar zuwa kwasa-kwasai maban-banta.

Ya kuma yaba ma babban kwamandan Makarantar, da sauran Jami’an sa, saboda namijin da suka yi har aka samu cigaban da aka samu zuwa yanzu, wanda Kuma ya yi fatan dorewar hakan a gaba.

Manjo Janar Aminu Bichi, ya sake nanata bukatar da ke akwai ga sabbin kwaratan sojin, su cigaba da dabbaka halayyan da aka koyar da su, da suka shafi biyayya da juriya da kishin Kasa da kuma duk wani nau’in abu da zai zama kan gaba a tafiyar da aikin su kamar yadda ya dace.

Tun farko da yake jawabin maraba, babban kwamandan Makarantar, Manjo Janar Sani Muhammed, ya ce, a duk bayan watanni shida, Makarantar na yaye kuratab Sojoji, da ake koyar da su dabarun yaki da basu horo na musamman domin fuskantar kalubalen tsaro ta ko’ina a fadin Nijeriya.

Sannan, ya taya sabbin Sojoji da ake yayewa a ranar 19 ga watan Oktoban nan murna, da kira garesu, na rike horon da suka samu daga Makarantar kamar yadda ya dace.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.