Labarai

Tinda China da Indiya suka cigaba, babu abinda zai hana Najeriya ci gaba – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babu abin da zai hana kasar ci gaba kamar kasashen China da India ko Indonesia. 

“Tun da China da India da Indonesia suka ci gaba, to babu abin da zai hana Najeriya ci gaba,” a cewar shugaban, wanda aka sake zaba karo na biyu a watan Fabrerun da ya gabata. 

Ya kara da cewa: “Kasashen China da Indonesia sun ci gaba karkashin tsarin mulkin mulukiya yayin da India ta kai gaci a karkashin tsarin demokuradiyya, a don haka muma babu abin da zai hana mu mu kai ga gaci”.

Shugaban na magana ne a ranar bikin murnar demokuradiyya, wacce a karon farko ake tunawa da ita a ranar 12 ga watan Yuni. 

An sauya ranar ne daga 29 ga watan Mayu domin tunawa da kuma rage radadin alhinin soke zaben shugaban kasa na 1993. 

Shugaba Buhari ya kuma sanar da sauya sunan filin wasa na Abuja zuwa Moshood Abiola, mutumin da aka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben na 1993 wanda gwamnatin sojin lokacin ta soke.

Wannan sanarwa dai ita ce ta fi birge wadanda suka halarci wurin taron idan aka yi la’akari da yadda wurin ya kaure da tafi bayan da ya ayyana hakan.

BBC Hausa

Masu Alaka

12 ga Juni: Mun ciyar da ‘yan makaranta fiye da miliyan 9 -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

To fa: Sanusi ya nemi Osinbajo yayi masa mataimakin shugaban kasa lokacin da Buhari bashi da lafiya

Muhammad Isma’il Makama

Ziyarar godiya muka kai wa Buhari – Ganduje

Dabo Online

Buhari ya hana Atiku wajen taro a Abuja

Dabo Online

Akwai yiwuwar sake komawa wa’adina na biyu da wasu tsofaffin Ministocina – Buhari

Dabo Online

Mun bawa gwamnonin jihohi cikakken taimako – Buhari

Dabo Online
UA-131299779-2