/

Kano: Kuri’ar da aka kama jabu ce, an buga ta domin koyar da zabe- Yan sanda

Karatun minti 1

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, karkashin jagorancin kwamishina Muhammad Wakili tace kuri’ar da aka kama yau a unguwar sabon gari jabu ce.

Rundunar tace a bincken data gudanar ta gano babu alamar da take nuna an dangwalawa jami’iyyar APC a jikin kuri’ar (Ballot Paper)

Mai magana da yawun rundunar na jihar Kano, DSP Haruna Abdallahi yace, za’ayi amfani da kuri’ar ne don koyawa mutanen jigawa yadda zaku kada kuri’arsu ba tare da bata ta ba.

An kama kuri’ar ne a kan hanyar ta zuwa jihar Jigawa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog