/

Malamai: In za su tsine min sau 1000, sai dai Allah ya karamin daukaka – Kwankwaso

Karatun minti 1
Kwankwaso
Tsohon gwamnan Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso, yayi karin haske akan maganarshi da yayi akan malamai da yace ya kamata su dena amfani da mambarinsu domin zagi ko kushe su.

A ziyarar da wasu malamai suka kai masa a ranar Alhamis, Kwankwason ya ce kowa yayi zagi a kasuwa yasan da wanda yake, ya ce su malaman da yake magana a kansu suma sun san da su yake.

“Irin wadannan malamai ko za su tsinemin sai dai Allah ya kara daukaka ni.

“Daya daga cikin abinda ya kawo wannnan muhawara shi ne rashin fadar sunaye ne, in an yi maganar masu shiga iri kaza, na ware wasu, da sauran wadanda ban fada ba. Kowa yasan a garin nan idan mukayi zagi a kasuwa mun san da wadanda muke.”

A kwanakin nan dai Sanatan ya yi magana da ta ja hankalin mutanen jihar Kano dama kasa baki daya akan shigar malamai siyasa su rika sukar wasu ‘yan siyasa . Lamarin da ya sa malamai da yawa yi masa raddi na cewa ya taba sunnar Annabi (S.A.W)

Sai dai wasu na ganin malaman su na sukar Kwankwason ne saboda bambancin ra’ayi, saboda wasu na cewa kar a zabi duka yan takarkarun da yake goyon baya.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog