Kano Pillars ta lashe kofin Aiteo na shekarar 2019

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta samu nasarar lashe kofin kalubale na Najeriya bayan ta doke kungiyar Niger Tornadoes a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

An dai tashi wasan canjaras inda kowacce kungiya bata zura kwallo ko daya ba har aka garzaya bugun fenareti.

An dai buga wasan ne a filin wasa na Ahmadu Bello dake Zaria a jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.

Dan wasan tsakiya na Kano Pillars, Rabi’u Ali Pele ne ya zama gwarzon dan wasa a wasan da kungiyar ta kara.

Masu Alaƙa  An samu raunuka da dama bayan farwa magoya bayan Kano Pillars a Katsina

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.