Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kano: Wasu matasa da makamai sun tarwatsa mutanen dake kan layin zabe a Gama – BBC HAUSA

1 min read

Shafin BBC Hausa ya rawaito cewa wasu matasa sun tarwatsa mutanen da suka hau layi domin kada kuri’arsu a mazabar Gama dake karamar hukumar Nassarawa a garin Kano.

BBC tace: “Bayan da aka yi layi don kada kuri’a a unguwar Gama sai aka kawo wasu dauke da sanduna da katakai suka nufi jama’a inda hakan ya sa kowa ya kama gabansa ake ta guje-guje.”

“A dai unguwar ta Gama a wasu wuraren mutane dauke da muggan makamai sun kori masu shirin yin zabe, inda kowa ya gudu gida domin tsira da rai.”

Madogara
©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.