Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kano: Zabe yayi nisa a mazabar Gama ta Kudu

1 min read

A cigaba da gudanar da karashen zaben gwamnan jihar Kano, daga mazabar GAMA ta Kudu, al’ummar yankin suna cigaba da kada kuri’arsu cikin lumana da kwanciyar hankali.

Gama ta Kudu na da rijisatar masu kada kuri’a kimanin mutum 2000, daga cikin 40,000 da mazabar GAMA take dashi baki daya.

Gidan Talbijin na NTA ra rawaito cewa zaben ya sha bambam da irin wanda ake gudanarwa a sauran gurare, domin jami’an tsaro sunyi dako a gaban makarantar da ake kada kuri’ar, inda suke hana kowa shiga sai masu kada kuri’a kawai.

Bidiyo
©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.