KANO: ‘Yan Sanda sun cafke Kwamishina a Kano bisa zargin tada tarzoma

Karatun minti 1

Hukumar yan sandan jihar Kano sun kama Kwamishinan Aiyuka na musamman, tsohon Ciyaman na karamar hukumar Birni, Hon Muntari Ishaq Yakasai.

Jami’an ‘yan sandan sun kame Ishaq a mazabar Yalwa dake karamar hukumar Dala.

Munyi kokarin jin ta bakin hukumar ‘yan sanda ta hannun mai magana da yawun ta, DSP Haruna Abdullahi amma hakan ya gaza cimma ruwa.

Sai dai shaidun gani da ido sun tabbatar da cafke kwamishinan kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog