1
Tsohon kwamishinan kula da ayyuka na jihar Kano, Engr Muazu Magaji ya kamu da Koronabairas.
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan da tsohon kwamishinan ya yi ‘murnar’ mutuwar Abba Kyari da cutar da Kwabid-19 ta zama ajalinshi.
DABO FM ta tattara cewar tin dai a ranar gwamnan Kano, Dr Ganduje ya saukeshi daga mukamin kwamishinan.
Tsohon kwamishina Mu’azu Magaji ya bayyana sakamakon kamuwa da cutar a shafinshi na Facebook a yau Alhamis da ake azumi na 14 a Najeriya.
Muazu Magaji ya bukaci da al’umma su taya shi da addu’ar samun waraka daga cutar da ta addabi duniya baki daya.
