Karfin wutar Lantarkin Najeriya ta ragu da 3,231MW

Karfin wutar lantarkin Najeriya ta ragu da 3,231 MW a ranar Laraba bayan mako daya na lalacewar na’ura.

Bayanai da suke fitowa daga matattarar bayanan kamfanin na ‘Transmission Company of Nigeria’ ya nuna cewa sunga karfin wutar ya koma 4,338MW da misalin karfe 6 na safe a 20 ga watan Afirilun 2019.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa matattarar kamfanin ta lalace a makon daya gabata.

Kamfanin ya shigar da 12,910.40MW; an samu ragowar 7,652.60; wutar na watsuwa a 8,100MW.

%d bloggers like this: