Karon farko cikin shekaru 10 a Zamfara, Matawalle ya kara wa Malaman Firamare 6,709 matakin aiki

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya karawa Malaman Firamare 6,709 girma a matsayinsu na ma’aikatan gwamnati.

DABO FM ta tattaro cewa; wannan ne karo na farko aka karawa malaman girma a cikin shekaru 10 kamar yacce Daily Trust ta tabbatar.

Gwamnan jihar, Matawalle, ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa wata ganawar siyasa da Sanata Hassan Nasiha, wakilin Zamfara ta tsakiya.

“Na rattaba hannu don karawa Malaman hukumar Ilimi girma saboda duba da mukayi a bayan korafin da suka shigar.”

“Gwamnatocin baya basa basu kulawa, amma duk da haka sukayi hakuri tare da fatan wata rana, masu share musu hawayensu zasu zo.”

“Zamewata Gwamna yana daga cikin amsa addu’ar da Allah Yayi domin share musu hawayen da suke dade suna zubarwa.”

Masu Alaƙa  Matawalle ya bi gidajen talakawa marasa karfi da tallafin ₦500,000 kowannen su

“Yanzu dukkanin zasu tafi matakin daya kamata suje na aiki domin su samu kwarin gwiwar cigaba da Ilimantar da ‘ya’yanmu su samu rayuwa mai kwai a gaba.”

Gwamnan ya kara jaddada kudurinshi na shayo kan duk wata matsala da take ciwa ‘yan jihar Zamafara tuwo a kwarya.”

DABO FM ta rawaito gwamna Matawalle yana cewa; “Bisa samun zaman lafiya a jiharmu, yanzu kuma zamu karkata wajen raya al’umma da yin shugabanci nagari.”

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.